Back

Gobara ta kashe yara ƙanana a sansanin ‘yan gudun hijira a Borno

A ranar Talata ne wata musiba ta afku a Borno yayin da gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke yankin Muna a jihar Borno.

Lamarin da ya faru a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri ya yi sanadiyyar rasa rayukan yara biyu.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba.

Kazalika, rundunar ‘yan sandan jihar Borno da gwamnatin jihar ba su ce komai ba kan lamarin.

Jihar Borno dai ta kwashe sama da shekaru goma tana fama da rikicin Boko Haram wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba mutane da dama da muhallansu.

Ƙarin bayani ba da jimawa ba…

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?