Back

Gobara ta lalata shaguna 50 da kayayyakin naira miliyan 360 a kasuwar Kwara

Wata gobara da ta tashi a kasuwar Owode da ke Offa a ƙaramar hukumar Offa a Jihar Kwara a ranar Talata, ta lalata dukiyoyin da ya kai naira miliyan 360.

An ruwaito cewa gobarar ta faru ne a sakamakon zubar da sigari da aka yi wanda ya ƙona kayan wuta a kasuwar.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatar da ɓarkewar gobarar a wata sanarwa da ya fitar.

Adekunle ya ce Hukumar Kashe Gobara ta samu labarin faruwar lamarin da ƙarfe 2:30 na safe, inda nan take ta tura jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin Oyeyipo James zuwa inda lamarin ya faru.

Ya bayyana cewa, haɗin kai da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta jiha da takwarorinsu na tarayya suka yi ya taimaka wajen shawo kan lamarin.

“Duk da ƙalubalen da aka yi fama da shi, an fafata na tsawon sa’o’i biyar kafin a kashe wutar gaba ɗaya, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin da ke kusa.

“Bincike na farko ya nuna cewa Kasuwar Owode, cibiyar kasuwanci mai ɗauke da shaguna 3,820 da tatuna 1,180, ta samu ɓarna kaɗan. Shaguna 50 ne kawai gobarar ta shafa, saboda saurin amsawa da matakan da Hukumar Kashe Gobara ta ɗauka.

“Darajar kayayyaki da kaddarorin da aka ceto daga ƙoƙarin kashe gobaran an ƙiyasta sun haura naira biliyan 12, wanda hakan ya kawo sauƙi sosai a cikin rikicin. Sai dai wannan mummunan lamari ya janyo asarar kayayyaki da suka kai naira miliyan 360.

“Bayan cikakken bincike, an tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne a sakamakon zubar da sigari da aka yi wanda ya ƙona kayan wuta a kasuwar, wanda ke nuna muhimmancin wayar da kai kan matakan kariya daga wuta,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?