Back

Gobara ta tashi a gidan tsohon Gwamnan Kano, Shekarau

Gobara ta ƙone wani ɓangare na gidan Mundubawa na tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau.

Gobarar ta auku ne da yammacin Lahadi, inda ta lalata falon matar Shekarau, Halima, amma ba a rasa rai ba.

An ruwaito cewa jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an kashe gobarar.

Ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin da ake cika wannan rahoto amma wata majiya ta iyali ta ce gobarar ta tashi ne daga ɗakin dafa abinci.

“Ina tsammanin gobarar ta tashi ne daga ɗakin girki na ciki. Mun gode wa Allah gobarar ta shafi ɗaya daga cikin ɗakunan Malam Ibrahim Shekarau ne kawai, kuma tuni jami’an hukumar kashe gobara suka yi ƙoƙarin kashe ta,” inji majiyar.

Mai baiwa Malam Shekarau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dakta Sule Ya’u Sule, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce gobarar ta tashi ne daga ɗakin girki na cikin gidan da ke ƙasan gidan.

Ya jaddada cewa, “mun gode wa Allah da cewa gobarar ta shafi ɗaya daga cikin ɗakin Malam Ibrahim Shekarau ne kawai kuma tuni jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar suka yi nasarar kashe gobarar.”

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Abdullahi yana wurin da gobarar ta auku yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai.

Ya ce ba zai iya yin tsokaci sosai kan duk wani abu da ya shafi gobarar ba a halin yanzu “saboda har yanzu muna ƙoƙarin ganin gobarar ba ta yaɗu zuwa wasu wurare ba.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?