
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci a gina makarantar sakandare ta ‘yan mata ta sojojin sama a Kano a matsayin cikamakin makarantar sakandaren maza da ke Kwa, Dawakin Tofa, a kan hanyar Kano zuwa Katsina.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature ya fitar, Yusuf ya yi wannan roƙo ne yayin ziyarar ban girma da Hafsan Hafsoshin Sojin Sama, Air Vice Marshal Hasan Bala Abubakar, ya kai gidan gwamnati a Kano.
Ya kuma nuna jin daɗinsa a bisa ƙwarewa da kuma tarihin Air Vice Marshal Abubakar, inda ya yaba da ƙoƙarin Rundunar Sojin Sama wajen magance matsalar tsaro, musamman wajen yaƙar masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga, da sauran masu aikata laifuka a Kano.
Gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafawa Rundunar Sojin Sama da kuma ‘yan uwa jami’an tsaro, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kan su wajen wanzar da zaman lafiya a Kano.
A martanin da Air Vice Marshal Abubakar ya mayar, ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da mamaye filin Rundunar Sojin Saman (NAF), inda ya buƙaci a maido da filin wanda aka sadaukar domin faɗaɗawa nan gaba.
Ya kuma nemi goyon bayan Gwamna Yusuf wajen haɗa cibiyar samar da ruwan sha ta Jihar Kano da gidan NAF domin inganta samar da ruwan sha.