Back

Gwamna Zulum ya raba naira miliyan 250 ga zawarawa da mata masu ƙaramin ƙarfi a Borno

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanya ido kan rabon naira miliyan 250 ga matan da mazajensu suka rasu da kuma marasa galihu 25,000 a ƙaramar hukumar Gwoza.

An gudanar da rabon kayayyakin ne a cibiyoyi huɗu da suka haɗa da Babban Filin Buga Wasanni, Makarantar Firamare ta Mega, Makarantar Sakandaren Gwamnati da Makarantar Sakandare ta Gwamnati, duk a cikin garin Gwoza.

Rabon a cewar Zulum, an yi shi ne domin tallafa wa matan da rikicin Boko Haram ya rutsa da su, waɗanda wasunsu suka rasa mazajensu sakamakon rikicin.

“Kimanin mata 25,000 ne suka ci gajiyar shirin rabon na yau kowaccen su ta samu naira 10,000 ta ƙaramin banki; mun buɗe musu asusu na banki,” inji Zulum.

Ya ƙara da cewa, “Da sannu a hankali, muna da niyyar rabawa a ɗaukacin ƙananan hukumomin 27 tare da tabbatar da cewa ɗimbin al’ummar suna da asusun ajiyar banki.

A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kai ziyarar duba aiki domin ganin yadda ake gudanar da aikin gina makarantar koyon aikin jinya da ke Gwoza.

Zulum, wanda ya bayyana gamsuwa da ingancin aikin, ya ba da umarnin kammala aikin da kuma amfani da shi nan da watanni shida.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?