Back

Gwamnan Bauchi ya nemi gafarar matar Tinubu kan barazanar kisa

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana barazanar kisa da aka yiwa uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a matsayin abin kunya na ƙasa.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne wani limamin Bauchi mai suna Sunusi Abubakar ya bayyana matar Shugaban Ƙasar a matsayin kafira da ya kamata a kashe a wani bidiyo, ko da yake daga baya ya janye kalaman nasa.

Gwamnan ya ba wa uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu haƙuri a jiya a fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu.

Gwamnan ya ce ya ji takaicin wannan barazanar amma uwargidan Shugaban Ƙasar ta nuna kanta a matsayin jajirtacciyar uwa da ta ziyarci jihar.

Mohammed ya ƙara da cewa: “A madadin Mai Martaba da kuma al’ummar Bauchi, muna ba da haƙuri kan wannan abin kunya na ƙasa, hakan ba zai sake faruwa ba.”

Mrs Tinubu, wadda ta je jihar ne domin ƙaddamar da Makarantar Sakandare da Cibiyar Fasahar Bayanai da Sadarwa, ta ce, “Ina so in gode wa mai girma gwamna da ya tabbatar min cewa ba abinda zai same ni, amma abin da na faɗa shi ne na tsufa da yawa in ji tsoro. Idan Allah ya ba ni shekara 60, ban ga ya kamata in ji tsoron mutuwa ba, amma na gode wa Allah da ya ba ni ƙarfin gwiwa na zo. Nijeriya ta mu ce kuma wannan lokaci ne da za mu haɗa kai fiye da kowane lokaci.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?