Back

Gwamnan Kano ya bayar da umarnin kama tsohon Sarki Ado Bayero

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin kama tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero wanda ya isa jihar da sanyin safiyar Asabar.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya isa Kano ne kwana guda bayan da gwamnatin jihar ta tabbatar da ƙudirin Majalisar Dokokin da ya soke kafa masarautu biyar a jihar.

Sanye da kayan sarki, Ado Bayero wanda ya isa filin jirgin saman Kano da misalin ƙarfe 5 na safiyar ranar Asabar, magoya bayansa sun yi masa kawanya.

Da yake magana daga baya ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a cikin wata sanarwa, Gwamna Yusuf ya ce, “Komawar da Aminu Ado Bayero ya yi zuwa Kano ba wani abu ba ne illa wani yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a da kuma ƙoƙarin lalata danƙon zaman lafiya da jihar ke samu.

“Don haka na umurci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar da ya kama Alhaji Aminu Ado Bayero, a duk inda aka gan shi a jihar.”

Tuni dai aka miƙa wa Sarki Lamido Sanusi takardar naɗin nasa da ke nuni da mayar da shi sarautar Sarkin Kano a hukumance ranar Juma’a.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?