Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya sanar da naɗin Alhaji Muhammadu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Kano.
Ya bayyana hakan ne bayan ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar da ta kafa masarautar Kano a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Alhamis.
Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne da misalin ƙarfe 5:10 na yamma tare da mataimakinsa da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da sauran manyan jami’an gwamnati.
A shekarar 2020 ne tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Sanusi daga karagar mulki, biyo bayan wata rashin jituwa tsakanin su.