Back

Gwamnan Kwara ya yi kira ga Musulmai da su zauna lafiya a Makkah

Gwamna AbdulRazaq AbdulRahman

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su nemi zaman lafiya da ci gaba a ƙasar nan.

AbdulRazaq ya yi wannan roƙo ne a cikin sakon da ya aika wa al’ummar Musulmin Nijeriya daga ƙasar Saudiyya, inda ya je Umara.

Malamin ya bayyana taron jama’a a masallacin Harami da ke Makkah a matsayin abin tunawa da haɗin kan al’ummar bil’adama da kuma buƙatar ganin an samar da zaman lafiya da ci gaba.

Ya ƙara da cewa “Babban taron da aka yi a ɗakin Allah mai albarka abin tunawa ne da haɗin kan al’ummar bil’adama da kuma buƙatar mu yi hakan a cikin ayyukanmu na yau da kullum domin samun zaman lafiya da ci gaba.”

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmin ƙasar nan da su yi amfani da damar ƙarshen watan azumin Ramadan domin neman albarkar Allah ga bil’adama, Jihar Kwara, Nijeriya, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da tawagarsa, da kowa da kowa.

“Lokaci ne na tunani da kuma lokacin neman albarkar Allah a kan bil’adama, jiharmu ta Kwara, Nijeriya, Mai girma Shugaban Ƙasa da tawagarsa, da kowa da kowa,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?