Back

Gwamnan Lagos Ya Amince Da Rage Kuɗin Sufuri, Ya Ba Wa Ma’aikatan Gwamnati Izinin Yin Aiki Daga Gida

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya amince da rage kashi ashirin da biyar cikin ɗari na farashin sufuri mallakar gwamnati.

Da yake jawabi ga al’ummar yankin kan matakan da gwamnatin shi ta ɗauka na magance wahalhalu, gwamnan ya ce gwamnatin shi ta kuma rage yawan kwanakin da ma’aikatan gwamnati ke yi daga ofis.

Ya ce ma’aikatan gwamnati daga mataki na ɗaya zuwa na sha huɗu za su yi aiki daga gida sau biyu a mako, yayin da aka bai wa ma’aikata daga mataki na sha biyar zuwa sha bakwai izinin yin aiki daga gida sau ɗaya a mako.

“Muna so mu fara da ma’aikatanmu, nan da nan daga mako mai zuwa, ma’aikatan ƙananan hukumomi za su riƙa aiki kamar sau uku a mako, matakin sha biyar zuwa sha bakwai kuma na iya aiki sau huɗu a mako,” inji shi.

“Ba wai za a rufe duk wani nau’in gwamnati ba ne. Za a tsara kalanda da tsara lokuta. Waɗanda ke matakin sha biyar zuwa sha bakwai ba za su yi aiki na kwana ɗaya ba.

“Raguwar kashi ashirin da biyar akan sufuri na tsarin Sufurin Jama’a na Jiha (bas, jirgin ƙasa, jirgin ruwa), zai fara ƙarshen wannan makon”, in ji shi.

Ya ce sauran nau’o’in ma’aikatan gwamnati da suka haɗa da malamai za su samu wasu nau’o’in tallafi domin su kasance a bakin aiki sau biyar a cikin mako guda.

Sanwo-Olu ya sanar da cewa jihar na jiran kayan abinci tirela ɗari uku, inda ya ƙara da cewa an samar da hanyoyin da za a tabbatar da kayayyakin sun isa ga waɗanda suke buƙata.

Ya ce gwamnati za ta gina cibiyoyin abinci guda huɗu domin samar da sabuwar hanyar rarraba abinci a jihar da kuma magance tashin farashin abinci.

“Za mu buɗe kasuwannin Lahadi a aƙalla kasuwanni arba’in a faɗin jihar Legas. Zaku iya siyan kayan abinci akan farashi mai rahusa. Za ku buƙaci kawai ku siya kayayyaki da darajarsu ta kai Naira dubu ashirin da biyar.”

“Haɗe da ɗaya a Idi-Oro, Mushin, ana kan gina wasu cibiyoyin abinci guda huɗu sannan kuma an gano wasu wurare guda bakwai a wasu ƙananan hukumomi domin a samar da ƙarin cibiyoyin abinci,” in ji shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?