Back

Gwamnan Zamfara ya fara biyan kudaden alawus na Naira biliyan 13.4, ga wadanda suka yi ritaya daga shekarar 2011.

Gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan Naira biliyan goma sha uku da miliyan 400 na kudaden tallafi ga wadanda suka yi ritaya a jihar. Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Zamfara kan harkokin yada labarai, Suleman Bala Idris ne ya bayyana a yau Asabar.

Gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai tantance bayanan ma’aikatan da suka yi ritaya domin biyan basussukan da suke bin gwamnati tun daga shekarar 2011 zuwa yau.

Idris, ya bayyana cewa wadanda suka yi ritayar da wadanda ke bin gwamnati bashin kuɗaɗen sallama tun a shekarar 2011, sun fara karbar kudaden su tun ranar alhamis da ta wuce.

“Gwamnatin jihar ta dauki wani muhimmin mataki na magance basussukan da ake bin ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda ya hada da na mutuwa, na wa’adin aiki, na sallama da na kwangila.

“Gwamna Dauda Lawal ya kafa wani kwamiti da zai tantance bayanan wadanda suka yi ritaya don daidaita basussukan da suka taru tun 2011.” Inji Suleman Idris 

“Bayan tantance bayanan ma’aikatan da suka yi ritaya, gwamnati ta gano cewa kudaden da ake bin jihohi da kananan hukumomi sun kai Naira biliyan 13.4.

“Kwamitin ya riga ya yi nisa da tara bayanai da tantance bayanan da kananan hukumomi da hukumar fansho ta jiha suka gabatar tare da tantance wadanda suka ci gajiyar aikin.

“Ma’aikatan jiha, da na kananan hukumomi da suka yi ritaya wadanda aka tantance sun fara karbar kudaden gratuity tun ranar Alhamis.

“Gwamnati za ta tabbatar da cewa duk wadanda suka yi ritaya an tantance su kuma an biya su ba tare da wata matsala ba.

“Gwamnatin jihar Zamfara na cika alkawarin da ta dauka na yiwa al’ummar Zamfara hidima ta hanyar ceto da kuma sake gina jihar domin samun ci gaba.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?