Back

Gwamnati Ba Ta Da Uzuri Kan Ƙarancin Abinci A Najeriya – Tsohon Minista

Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Sanata Adeseye Ogunlewe, ya ce gwamnati ba ta da wani uzuri kan matsalar ƙarancin abinci da ake fama da shi a ƙasar nan.

A yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, Ogunlewe ya bayyana damuwar shi game da halin da ƙasar ke ciki a yanzu, amma ya ce bai yi mamaki ba.

Ya zargi gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yin sakaci a fannin ilimi musamman jami’o’i da masu bincike da ya kamata su yi bincike da bunƙasa hanyoyin noma na zamani.

Ya ce shekaru takwas gwamnati tana yaƙi da hukumomin ilimi, ta rufe jami’o’i, tare da hana su tallafin bincike.

Ogunlewe, wanda lauya ne kuma tsohon Sanata mai wakiltar Legas ta Gabas, ya ce babu wata ƙasa da za ta iya ci gaba ba tare da bincike ba.

Ya koka da cewa malaman jami’o’in ba su da hannu a harkar noma, saboda babu kuɗin bincike, inda ya ce Najeriya na da jami’o’i da kwalejojin aikin gona sama da ashirin, tare da fadin ƙasa na waɗannan makarantu duka kusan hekta dubu hamsin.

Ya ce, “Na damu matuƙa da abin da ke faruwa a ƙasar nan, amma ban yi mamaki ba, domin tsawon shekaru takwas na gwamnatin da ta gabata, ana yaƙi ne da jami’o’i, da masu bincike, da mutanen da ya kamata su yi wa ƙasarku bincike don samun hanyoyin noma na zamani. Amma kun yaƙe su, kun rufe jami’o’i. Babu bincike. Babu tallafi.

“Babu wata ƙasa da ke ci gaba ba tare da bincike ba saboda kayayyakin gona sune kayayyakin da za ku iya fitarwa ƙasashen waje. To amma me ya sa malaman jami’o’i basu da hannu a ciki? Babu kuɗi don bincike.

“Muna da jami’o’i da kwalejojin aikin gona sama da ashirin. Kuma faɗin ƙasan wadannan makarantu duka kusan hekta dubu hamsin ne. Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Abeokuta kaɗai tana da kusan hekta dubu goma. Amma babu wani saka hannun jari a cikinsu, duk da cewa sun dogara sosai kan bincike. “

Ogunlewe ya kuma buƙaci gwamnati mai ci da ta saka hannun jari a makarantu da bincike na noma, inda ya ce Najeriya ba ta da uzuri na ƙarancin abinci, tare da duk wani albarkatu da kuma ƙarfin da take da shi.

Ya ce bincike da ƙirƙire-ƙirƙire sune jigon magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki, da inganta samar da abinci da ci gaban tattalin arziƙi.

“Don haka, ya kamata gwamnati ta saka hannun jari a cikinsu. Ba mu da wani uzuri na ƙarancin abinci a ƙasar nan, tare da duk waɗannan cibiyoyi da muke zuba jari a cikinsu tsawon shekaru,” inji shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?