Back

Gwamnati na za ta rage hauhawar farashin kayayyaki, inji Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Nijeriya da kada su damu da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, yana mai shan alwashin cewa gwamnatinsa za ta rage shi.

Shugaban Ƙasar ya ce duk da cewa ba shi da wani siddabaru don magance matsalar tattalin arziƙin ƙasar, bai kamata ‘yan ƙasar su damu ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugabannin Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC na buɗa baki a watan Ramadan na 2024 a fadar gwamnati da ke Abuja.

Nijeriya dai na fama da matsalar tattalin arziƙi sakamakon hauhawar farashin kayayyaki tun bayan da gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur tare da haɗe farashin canji a shekarar 2023.

Rahoton ƙarshe na wannan shekara ta 2024, daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tashi daga kashi 29.9 cikin 100 a watan Janairu zuwa kashi 31.7 cikin 100 a watan Fabrairu.

Da yake magana kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi, Tinubu ya ce, “Aiki ne mai wahala da kuka yi wa al’ummar Nijeriya alƙawari a lokacin da kuke yi mani yaƙin neman zaɓe, kun yi musu alƙawarin samun sakamako mai kyau. Ko baku yi ba? Shi ke nan! Dole ne in yi aiki don shi. Babu wani siddabaru.

“Na yi yaƙin neman zaɓe bisa fata, dole ne in yi aiki don wannan fata don farin cikin kowannenmu.

“Tattalin arziƙin ƙasar yana da kyau. Kar ku damu da wannan… mun san muna da ƙalubalen hauhawar farashin kayayyaki, ba damuwa, za mu rage shi.”

“Ba wai sai mun je can mun ɗauke su aiki domin su yi mana aikin ba, da kanmu zamu yi. Duk abin da ke faruwa da mu, dole ne mu magance shi da kanmu. Yunƙurinku, tunaninku, hazaƙar ku, jarinku, sadaukarwa da aiki tuƙuru ne kawai zai iya kaimu can.”

‘Yan Nijeriya na fuskantar ƙalubale daban-daban a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da suka haɗa da tashin farashin abinci, faɗuwar darajar naira, da kuma sanarwar ƙarin kuɗin wutar lantarki ga abokan kasuwancin Band A a kwanan nan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?