Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi wa fursunoni 96 afuwa a gidajen gyaran hali daban-daban a faɗin jihar bisa haƙƙin sa na jinƙai.
Gwamnan ya bayar da gudunmawar naira miliyan 13 da za a raba a tsakaninsu a matsayin kuɗin sufuri da kuma abubuwan jin ƙai domin su fara ƙananan sana’o’i da kuma wasu naira miliyan 7 domin biyan tarar su kamar yadda kotuna ta yanke musu hukunci.
Mohammed ya ce ya yanke shawarar yin afuwar ne biyo bayan rahoton Kwamitin Bayar da Shawara kan Jinƙai na cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun sauya sheƙa, inda ya ce waɗanda ke da ƙananan laifuffuka ne kuma waɗanda ba za su iya biyan tarar da aka yi masu ba kawai aka zaɓa don shirin afuwar.
Gwamnan ya bayyana cewa ya ƙi yin afuwa ga waɗanda suka aikata manyan laifuka domin kar a kwaɗaitar da aikata irin waɗannan laifuka.
Mohammed ya sanar da cewa kowanne daga cikin fursunonin da aka yi wa afuwa zai samu kuɗi naira 100,000 domin fara wata sabuwar sana’a don dogaro da kansu da kuma zama ‘yan ƙasa nagari.
Tun da farko, Shugaban Majalisar ba da Shawara kan Jinƙai ta Jiha, wanda shi ne Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a, Hassan U. EI-Yakub (SAN), ya bayyana cewa majalisar ta samu jimillar roƙo 106 daga waɗanda aka yankewa hukuncin ɗaurin rai da rai suna neman gwamna ya ji ƙansu ya musu afuwa.