Back

Gwamnatin Borno ta ba da tallafin naira biliyan 1.3 ga ɗaliban jinya da ungozoma 997

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ware naira biliyan 1.3 na ɗaliban jinya da ungozoma 997 waɗanda ‘yan asalin jihar ne.

Gwamnan ya bayyana hakan ne jiya a yayin ƙaddamar da shirin bayar da tallafin karatu a Maiduguri.

Ya ce da farko shirin ya samu ‘yan takara 1,080, inda aka zaɓo ‘yan takara 40 daga kowace ƙaramar hukuma 27.

Bayan jarrabawar shiga, an zaɓi ‘yan takara 997 da suka yi nasara don cin gajiyar tallafin.

Zulum ya jaddada cewa wannan shiri na da nufin magance ƙaruwar buƙatar ma’aikata na ayyukan kiwon lafiya saboda ƙaruwar al’ummar jihar.

Ya ƙara da cewa kasafin kuɗin tallafin ya haɗa da naira miliyan 124,149,000 na kuɗin makaranta, yayin da za a biya sauran naira miliyan 1,181,040,000 a matsayin alawus na naira 30,000 duk wata ga kowane ɗalibi a duk tsawon karatunsa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?