Back

Gwamnatin Dubai ta fara gina tashar filin jirgin sama ‘mafi girma a duniya’

Zanen sabon tashar a Filin Jirgin Saman Al Maktoum

Gwamnatin Dubai ta ba da sanarwa a ranar Lahadi cewa ta fara gina wani sabon tasha a Filin Jirgin Saman Al Maktoum, wanda zai zama “mafi girma a duniya” a kan kusan dala biliyan 35.

Shugaban Dubai kuma Firayim Ministan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum ya ce “Mun amince da zanen sabon tashar fasinja a Filin Jirgin Saman Al Maktoum, kuma mun fara ginin a kan kuɗi AED biliyan 128 (dala biliyan 34.85).

Da zarar ya fara aiki, filin jirgin zai “ba da damar ɗaukar fasinjoji miliyan 260 a duk shekara”, inji gwamnatin a cikin wata sanarwa.

Sheikh Mohammed ya ce zai kasance “mafi girma a duniya” kuma zai kasance “ninki biyar na girman Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Dubai na yanzu”, wanda yana ɗaya daga cikin manyan filayen jiragen sama a duniya.

A cewar Sheikh Ahmed bin Saeed Al Maktoum, Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Dubai, kuma Shugaban Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na Emirates, “za a kammala kashi na farko na aikin cikin shekaru 10, tare da ƙarfin ɗaukar fasinjoji miliyan 150 a duk shekara.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?