
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da naira biliyan 1.1 don sayan ƙarin kayan abinci cikin gaggawa da suka haɗa da buhunan shinkafa 12,000 da kwalayen taliya 15,000 domin sayarwa ma’aikatan gwamnati kan farashi mai rahusa.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa ta Jiha (SEC) a ranar Litinin.
Ya ce siyan kayan abincin na daga cikin shirin gwamnatin jihar na samar da shaguna na haɗin gwiwa a dukkan ƙananan hukumomin jihar 27 domin sayar da kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki ga ma’aikatan gwamnati kan farashi mai rahusa.
Sagiru ya bayyana cewa tuni aka samar da hanyoyin kafawa da gudanar da shagunan haɗin gwiwa inda ma’aikatan gwamnati za su iya karɓar bashin kayan abinci, sannan su biya bashin kashi-kashi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa an kashe naira biliyan 2.8 a shirin ciyarwa na watan Ramadan na bana.