Back

Gwamnatin Kaduna ta raba kayayyakin noma ga manoma 40,000

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, a ranar Litinin ya ƙaddamar da rabon kayayyakin noma da na sarrafa amfanin gona ga ƙananan manoma 40,000 a wani shirinsa na ‘A Koma Gona.ʼ

Taron wanda aka yi don bikin cikar sa shekara ɗaya a kan karagar mulki ya gudana ne a ƙaramar hukumar Ikara, inda aka mayar da hankali kan waɗanda suka ci gajiyar shirin a shiyyar Sanatan Arewa.

Gwamna Sani ya bayyana Kaduna a matsayin jihar da ke kan gaba wajen noman citta, masara, da tumatur a Nijeriya, sai dai ya nuna damuwarsa kan asarar da ake samu bayan girbi, musamman a amfanin gona mai saurin lalacewa kamar tumatur.

Don magance hakan, gwamnan ya yi alƙawarin sake duba shirin da aka yi watsi da shi a baya na kafa kamfanin sarrafa tumatur a Ikara, da nufin rage asarar da manoman yankin ke fuskanta.

Da yake jawabi ga al’ummar manoman, Gwamna Sani ya jaddada muhimmancin aikin noma a fannin tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi da ɗorewar rayuwa.

Ya ce ƙananan manoma da masu sana’ar sarrafa kayan amfanin gona na kokawa saboda ƙalubalen da ake fuskanta na tattalin arziƙi.

Gwamna Sani ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kayan aikin da aka samar da su yadda ya kamata.

Kwamishinan Noma, Murtala Dabo, ya ce matakin da gwamnan ya ɗauka ba wai kawai zai inganta samar da abinci a Kaduna da kuma faɗin Nijeriya ba, har ma zai taimaka sosai wajen farfaɗo da tattalin arziƙin karkara.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?