
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da tallafin naira 500,000 ga kowanne daga cikin maniyyatan jihar.
Tallafin ya biyo bayan umarnin da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta bayar, inda ta buƙaci maniyyatan da su biya ƙarin naira miliyan 1.9 na kuɗin Hajjin shekarar 2024.
Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Ɗan Baffa, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Laraba a Kano.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta biya jimillar kuɗi naira biliyan 1.4 ga maniyyata 2,096 da suka yi rijista.
Ya ce gwamnatin jihar Kano ta ɗauki wannan matakin ne duba da ƙarin kuɗin aikin Hajji da NAHCON ta yi a baya-bayan nan wanda aka danganta shi da rashin daidaiton canjin dala.
“Mun yi la’akari da matsalolin tattalin arziƙi da mutane ke fuskanta a halin yanzu kuma ƙarin kuɗin aikin Hajji babban ƙalubale ne ga ɗimbin maniyyata. Don haka ne muka ɓullo da shirin bayar da tallafin don rage raɗaɗin da ke addabar maniyyatan,” inji babban daraktan.
Ɗan Baffa ya ƙara da cewa da wannan tallafin maniyyatan da suke son zuwa yanzu za su biya naira miliyan 1.4 maimakon naira miliyan 1.9.
Ya ce an ba da tallafin ne kawai ga waɗanda suka biya kuɗin aikin Hajji na farko na naira miliyan 4.7 kuma aka yi musu rijista.
“Ina so in bayyana cewa tallafin ya kasance ne ga maniyyatan mu 2,096 da suka yi rajista da suka biya ɓangaren kuɗin ga hukumar. Amma ana buƙatar sabbin maniyyata da su biya naira 8,254,464.74 a matsayin cikakken kuɗin aikin Hajjin bana kamar yadda Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta buƙata”.
Alhaji Baffa ya buƙaci dukkan maniyyatan da suke son zuwa aikin Hajji da su tabbatar sun biya sauran kuɗaɗen kafin ranar 28 ga Maris, 2024 kamar yadda NAHCON ta umarta.
Ya buƙaci NAHCON da ta ƙara wa’adin biyan kuɗin domin maniyyata su samu isasshen lokacin da za su biya ƙarin kuɗin.
“Ina roƙon hukumar NAHCON da ta roƙi mahukuntan Saudiyya da su ƙara wa’adin domin ‘yan Nijeriya da dama su samu halartar aikin hajjin bana,” inji shi.