Back

Gwamnatin Kano ta gurfanar da Ganduje, matar sa, da wasu kan zargin laifuka guda 8

Ganduje da matarsa

Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje, bisa zargin aikata laifuffuka guda takwas da suka haɗa da karɓar dala 200,000 daga hannun wani ɗan kwangila.

A cikin takardar tuhumar da aka shigar a gaban Babbar Kotun Kano, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin NNPP ta ce laifin ya ci karo da dokar Hukumar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano ta shekarar 2008.

Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lesaga General Enterprises.

Gwamnatin Jihar ta kuma zargi Ganduje da karɓar kuɗi dala 210,000 daga “mutane da hukumomin da ke nema ko aiwatar da kwangilar Gwamnatin Jihar Kano da ko aikin gyaran kasuwar masaƙu ta Kantin Kwari a matsayin cin hanci ta hannun ɗaya daga cikin ‘yan kwangila (wakili)”.

Ganduje da na kusa da shi sun yi ta musanta zargin, inda suka ce an haɗa faifan bidiyon ne domin a ɓata sunan tsohon gwamnan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?