
Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) sun musanta cewa ana shirin mayar da kudaden gida na Dala biliyan 30 zuwa Naira.
Wannan wani martani ne ga rahotannin da ke cewa gwamnatin tarayya da babban bankin kasar na tunanin sauya asusun gida zuwa naira a wani mataki na magance matsalar canjin kudaden waje da kuma dakatar da faduwar darajar naira.
Wannan bayanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da ministan kudi da kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin Najeriya, Wale Edun, suka fitar ranar Asabar, inda ya ce babu gaskiya a cikin rahoton, ya kuma yi watsi da labarin a matsayin karya.
Haka kuma babban bankin, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) a ranar Asabar 3 ga Fabrairu, 2024, ya bayyana rahoton a matsayin na bogi.
Abin da Gwamnatin Najeriya da babban bankin ke cewa:
Edun a cikin bayaninsa ya ce satar rahotannin karya ne Kawai da yunkurin kawo cikas ga tattalin arzikin kasa, ya Kara da cewa babban bankin shi ne kawai wanda aka keɓe don sauye-sauyen manufofin kuɗi kuma a koyaushe zai ba da shawara kan kowane canjin manufofin kan harkokin kudade kafin a kawo su, su fara aiki.
”Babban bankin a bude yake domin amsa tambayoyi game da manufofin mu”.
Yace, babu gaskiya a ikirari da jaridar Punch ta wallafa na cewa gwamnatin tarayya na shirin sauya kudaden kasashen waje a asusun ajiyar masu ajiya zuwa naira.
“Buga irin wannan karya. a dai dai lokacin da gwamnati ke kokarin dawo da daidaituwar tattalin arziki da kuma amincewa da kudin kasar tamkar zagon kasa ne ga tattalin arziki.
“Don kaucewa shakku, ina jaddada cewa kudaden kasashen waje na masu ajiya a cikin asusun su na gida ba za a sauya su zuwa naira ba.”
Babban bankin a sakon da, ya ce:
“Babu wani shiri na sauya asusun gida na dala biliyan 30 zuwa naira. Wannan labarin karya ne!’’
Rahotanni ne Kawai da ke da nufin haifar da firgici a cikin kasuwar forex.
Mukaddashin Daraktan Sadarwa na babban bankin, Mrs. Hakama Sidi-Ali, a wata sanarwa da ta fitar ta bayyana zargin a matsayin karya da nufin haddasa firgici a kasuwar canji.
Ta ce, ‘’babban bankin Najeriya (CBN) ya hankalta kan wani labari da wata jarida ta kasa ta buga na cewa gwamnatin tarayya na tunanin sauya kudaden gida da suka kai dala biliyan 30 zuwa Naira.
‘’Wannan zargi kwata-kwata karya ne kuma yana da nufin tayar da firgici a kasuwar canji, wanda bankin ke kokarin daidaitawa, kamar yadda ayyukan sa da manufofin sa suka tabbatar.