Hukumar kula da gasa da masu sayayya ta tarayya, FCCPC, ta bude babban ofishin babban kantin sayar da kayayyaki na Sahad, wanda ya rufe a ranar jumma’a da ta gabata saboda karbar Kuɗaɗen mutane da rashin gaskiya wajen kayyade farashin.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, mukaddashin shugaban hukumar, Dakta Adamu Abdullahi, ya ce sake bude kasuwar ya biyo bayan fahimtar juna da jajircewa daga kantin sayar da kayayyakin da cewa zasu aiwatar da tsarin farashi na gaskiya.
A cewar shi, hukumar na sane da cewa ana iya samun irin wannan abu na banbanta farashin sauran kayyaki da masu siye ke bukata cikin sauri a fadin kasar nan.
Ya shawarci manyan kantuna ko kantuna masu yi wa kwastomomi kwace da su daina irin waɗannan ayyukan domin guje wa hukunci.
“Ana sa ran ‘yan kasuwa za su nuna bayanan farashi na gaskiya don ƙarfafa wa masu siye gwiwa domin yin soyayya vikin wayewar kai akan farashi musamman a lokutan kalubalen tattalin arziki.
“Hukumar, ta ci gaba da jajircewa wajen yakar duk wani nau’i na cin zarafi ko yaudara da ke lalata haƙƙin mabukaci,” in ji shi.
Hukumar ta rufe babban kantin ne a ranar Juma’a saboda karbar Kuɗaɗen masu siye – siye ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin fayyace farashin kayayyaki.