Back

Gwamnatin Najeriya ta sabunta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci daga Nijar zuwa Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sabunta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya da kuma daga Najeriya zuwa can.

Wannan wani bangare ne na kudurorin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) kan Jamhuriyar Nijar, domin Saka mata takunkumi bisa juyin Mulki da soja suka yi a ranar 26 ga watan Yuli, na shekarar bara wanda suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum inda suka maye gurbinsa da gwamnatin mulkin soja da aka dora Janar Abdourrahamane Tchiani a matsayin Shugaban kasar.

Takunkumin ya hada da umarnin cewa babu wani jirgin kasuwanci daga Nijar da zai wuce sararin samaniyar Najeriya kuma babu wani jirgin da ya fito daga Najeriya da zai wuce sararin samaniyar Nijar.

Wannan umarnin na (Notice to Airmen (NOTAM)) na kunshe ne a cikin wata wasika mai daga Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya mai sanye da  kwanan wata 2 ga watan 2 na wannan shekarar wadda kuma Daraktan Kula da zirga-zirgar Jiragen Sama, Tayo John ya sanya wa hannu, a madadin Manajan Darakta da Babban Jami’in Hukumar.

Wasikar ta bayyana cewa, “A bisa kudurin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, an dakatar da dukkan jiragen kasuwanci daga Nijar zuwa Najeriya, ko daga Najeriya zuwa Nijar. 

Sai dai wasikar ta kara da cewa, “Wadannan hane-hane ba su shafi: (a) Jirgin sama da ya wuce ta sararin samaniyar Nijar; (b) Jirgin sama a cikin yanayin gaggawa da (c) jirage na musamman.”

Ya kuma ba da umarnin cewa “jirage na musamman za su sami izini daga sakatare na dindindin na Ma’aikatar Jiragen Sama da sararin samaniya.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?