
Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto
A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Sokoto ta ce za ta kashe naira biliyan 6.7 wajen ciyarwa da watan Ramadan.
Shirin ya haɗa da rabon hatsi da kuma samar da abinci a cibiyoyin ciyar da abinci.
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana haka a lokacin ƙaddamar da rabon hatsi ga marayu 18,400 da gajiyayyu a faɗin jihar.
Ya ce kowanne daga cikin marayu 18,400 da marasa galihu za su karɓi buhunan shinkafa da gero da tsabar kuɗi naira 5,000.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya gode wa gwamnatin jihar kan yadda ta ci gaba da gudanar da shirin ciyarwa da watan Ramadan.
Sarkin ya baiwa gwamnan tabbacin goyon bayansa a ƙoƙarinsa na inganta rayuwar jama’a.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tausaya wa mabuƙata.