
Gwamnatin Tarayya ta kammala tattaunawa da masu saka hannun jari daga ƙasar Netherlands don samun tallafin Yuro miliyan ashirin da biyar don gina gadoji masu muhimmanci a Najeriya. Hakan ya bayyana a ranar Asabar.
Bayan ganawar shi da tawagar masu zuba jari daga ƙasar Netherlands, ƙarƙashin jagorancin Jakadan Najeriya a ƙasar, Oluremi Oliyide, a Abuja, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana ƙudurin gwamnati na samun damar shiga tsakani na ƙasa da ƙasa daga ƙungiyoyin masu ba da tallafi da abokan hulɗar ci gaba don tunkarar matsalar ƙarancin ababen more rayuwa da ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziƙi a Najeriya.
A cewar wata sanarwa da mai baiwa Ministan shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Uchenna Orji ya fitar, matakin da gwamnati ta ɗauka ya dace da shirin nemo sabbin hanyoyin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, kamar yadda gwamnatin Sabunta Fata ta Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta tsara.
Ministan ya jaddada muhimmancin faɗaɗa ƙawance da haɗin gwiwa don tallafawa sassa masu muhimmanci na tattalin arziƙi. Hakan zai samar da ingantaccen ci gaban tattalin arziƙi.
Yayin da yake tabbatar wa masu zuba hannun jarin cewa da zarar an gudanar da bincike tare da gabatar wa shugaban ƙasa takardar neman amincewa, Umahi ya ce, “Muna da ayyuka da dama da za mu iya yi tare.
“Amma ina ganin mafi kyawun abin da za a yi shi ne a kammala wannan, wanda shine tallafi, sannan a fara aiwatar da aikin, kuma a wurin yarjejeniya da zaɓan ayyuka, za mu koma ga Shugaban Ƙasa don amincewarsa.”
Tun da farko a nasa jawabin, Jakadan Najeriya a Netherlands ya ce tawagar ta zo Najeriya ne domin tattaunawa kan tayin tallafin Yuro miliyan miliyan ashirin da biyar da Janson Bridging International ta yi don saka hannun jari kan ababen more rayuwa a Najeriya.
An ambato wakilin yana cewa, “Janson Bridging shi ne kamfanin ƙera gada mafi girma a nahiyar Turai kuma kamfanin hayar gada mafi girma a duniya.”
Ya yi alƙawarin taimakawa wajen hanzarta aiwatar da yarjejeniyar a ɓangaren kamfanin da zaran an kammala dukkan tsare-tsare.
A nasa ɓangaren, ɗan tawagar kuma Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Kasuwanci na Ƙasa da Ƙasa, Eric Okunde, ya ce masu zuba jarin a shirye suke da wannan shawara kuma a shirye suke don yin aiki tare da Ma’aikatar Ayyuka wajen aiwatarwa.