Back

Gwamnatin Tarayya na son a rushe hukumomin zaɓe na jihohi

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayar da shawarar soke Hukumomin Zaɓe Masu Zaman Kansu na Jihohi (SIECs).

Ya ce a mayar da ayyukansu ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin tabbatar da ‘yancin kai da gaskiya a sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi.

Da yake jawabi jiya a Abuja a wajen Taron Ƙasa kan Matsalar Tsaro da Shugabanci Nagari a Nijeriya a Matakin Ƙananan Hukumomi wanda Majalisar Wakilai ta shirya mai taken, ‘Matsalar Tsaron Nijeriya da Shugabanci Nagari a Matakin Ƙananan Hukumomi,” Fagbemi ya ce soke hukumomin zaɓe na jihohi zai ba da damar dimokaraɗiyya ta samu gindin zama a ƙananan hukumomi ta hanyar gyara tsarin mulkin ƙasar.

Ya ce yin hakan zai kawar da duk wasu matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban ƙananan hukumomi da kuma iya gudanar da ayyukansu da tsarin mulki ya amince da su.

Ya ce, “Don cimma wannan, masana da dama sun ba da shawarar cewa akwai buƙatar a soke hukumomin zaɓe masu zaman kansu na jihohi.

“Ya kamata a mayar da ayyukansu da ikonsu ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta saboda hukumar zaɓe mai zaman kanta na jiha ta kasance abin dogaro ga kowane gwamna mai ci. Ana ganin wannan shi ne ummul haba’isin matsalar shugabancin ƙananan hukumomi a Nijeriya”.

Ya ce duk da tanade-tanaden tsarin mulki na tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomi, a ko da yaushe gwamnatocin jahohin suna ruguzawa ko soke ƙananan hukumomi ba bisa ƙa’ida ba.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?