Back

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin titin jirgin ƙasa na Fatakwal zuwa Aba

Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali

Ministan Sufuri, Sanata Saidu Alkali, a ranar Talata ya ƙaddamar da aikin titin jirgin ƙasa na Fatakwal zuwa Aba.

Wannan ci gaban ya zo ne bayan wasu yunƙuri biyu da suka yi rashin nasara a baya na fara aiki akan titin.

Da yake jawabi ga mutanen da suka haɗa da manyan sarakunan gargajiya daga Jihar Ribas, Alkali ya bayyana mahimmancin aikin titin a matsayin wuraren da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke baiwa fifiko.

Alkali ya bayyana cewa titin zai haɗa muhimman tashoshi kamar su Onne, Bonny, da kuma Fatakwal, wanda zai sauƙaƙa jigilar kayayyaki ta hanyar gabas.

Ya ƙara da cewa, “fara gudanar da ayyuka a wannan ɓangare na aikin na da nufin bunƙasa harkokin tattalin arziƙi tsakanin yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Za mu ci gaba da jajircewa wajen ganin ɗan kwangilar ya yi gaggawar kammala hanyar Aba-Enugu, da ƙara haɓaka alaƙa da bunƙasar tattalin arziƙi a yankin.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?