
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 29 ga Maris da kuma Litinin 1 ga Afrilu a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Ista.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Aishetu Ndayako a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ranar Laraba a Abuja.
A cewarta, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.
Tunji-Ojo ya buƙaci Kiristoci da dukkan ‘yan Nijeriya da su yi koyi da sadaukarwa da kauna da Yesu Almasihu ya nuna wajen mutuwa domin fansar mutum.
Ministan ya yi nuni da cewa, bikin Ista ya wuce ma’anar addini, yana inganta ɗabi’un soyayya, afuwa da jin ƙai waɗanda suke da muhimmanci ga haɗin kai da zamantakewa.
Ya yi kira ga Kiristoci da su yi koyi da waɗannan kyawawan halaye domin suna iya yin tasiri mai kyau ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙin Nijeriya ta hanyar samar da haɗin kai, rage rikice-rikice da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ‘yan Nijeriya.
Tunji-Ojo ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su nuna ayyukan jin ƙai da karamci don taimakawa wajen rage wa marasa galihu daga cikin su halin rayuwa.
Wannan, in ji shi, ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya kuma yi wa kiristoci na gida da waje murnar zagayowar ranar Ista.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa kai da gwamnatin Tinubu a ƙoƙarinta na kawo ci gaba mai ɗorewa da kuma samar da wadata ga kowa da kowa.