Back

Gwamnatin Tarayya ta ba da tallafin kuɗin aikin Hajji naira biliyan 90

Gwamnatin Tarayya ta fitar da kuɗi naira biliyan 90 domin tallafawa aikin hajjin 2024.

Wata majiya mai tushe daga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis.

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce idan ba haka ba, da an buƙaci kowane maniyyaci da ya ƙara aƙalla naira miliyan 3.5 a kan kuɗin da aka fara biya da ya kai naira miliyan 4.9.

Wani babban jami’i a Fadar Shugaban Ƙasar ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya “da gaske ta ba da wasu tallafin kuɗi don aikin hajji”.

Majiyar NAHCON ta shaida cewa da hukumar ta samu naira biliyan 230 a matsayin tallafi daga Gwamnatin Tarayya, da ba a buƙaci maniyyatan su ƙara ko kwabo ba.

“Matsalar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje ya haifar da matsaloli da yawa. Don haka ne Hukumar Alhazai ta buƙaci maniyyatan su biya ƙarin kuɗi naira miliyan 1.9 kowanne. A gaskiya hukumar ta buƙaci naira biliyan 230 don daidaita bambance-bambancen kuɗin tafiya da matsalar canjin kuɗi ya haifar.

“Tallafin naira biliyan 90 da gwamnati ta bayar an sanar da shi ne a gaban ‘yan jarida a lokacin ƙaddamar da hukuma da masu gudanarwar NAHCON da aka gudanar a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa a ranar 28 ga Fabrairu, 2024.

Amma su (’yan jarida) an nemi kar su ba da rahoton. Shi ya sa babu wata jarida da ta ɗauki rahoton. Ko kun gani a cikin wani rahoto?”

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Idan maniyyata suka biya naira miliyan 1.9, to za a iya daidaita su.”

Ya ce NAHCON ta kuma tuntuɓi gwamnonin jihohi “domin su ba da tallafin kuɗin aikin hajji ga maniyyatan da ke jihohinsu. Kano ta mayar da martani inda ta biya naira 500,000 ga kowane maniyyaci.

“A lissafin da aka yi a baya, naira biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar zai iya tallafawa maniyyata 19,000 ne kawai da naira miliyan 3.5. Amma idan aka raba shi a kan maniyyata 50,000, an rage shi zuwa naira miliyan 1.9; ma’ana Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa kowane maniyyaci da naira miliyan 1.6 kafin kowane maniyyaci ya cika sauran naira miliyan 1.9,” inji shi.

Wata majiya daga fadar Shugaban Ƙasa, ta ce gaskiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da abin da ya kira “babban tallafin kuɗi” don gudanar da aikin hajjin bana.

Da aka tambaye shi ko Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗi har naira biliyan 90 a matsayin tallafi ga aikin hajjin, sai kawai jami’in ya ce: “wataƙila hakan bai yi nisa da gaskiya ba.”

Ya ƙara da cewa, “Tabbas Gwamnatin Tarayya ta bayar da tallafi ga maniyyatan saboda maniyyatan suna ta kuka.

“A ƙa’ida, duk wani tallafi da gwamnati za ta bai wa kowane addini, ko addinin Kirista ko na Musulmi, gwamnati ba ta son bayyana hakan a fili don kada ya zama kamar gwamnati tana nuna fifiko ga wani addini.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?