Back

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin a gaggauta sakin tan 102,000 na shinkafa da masara

Matsalar ƙarancin abinci da ake fama da ita a ƙasar Najeriya, haɗi da hauhawar farashin kayayyaki sun tilastawa gwamnatin tarayya bada umarnin sakin shinkafa da masara tan 102,000 ga ‘yan kasar.

Gwamnati ta kuma bayyana cewa za ta iya shigo da duk wani giɓi da za a iya samu don ƙara kayan masarufin.

Ministan Yaɗa Labarai, da eayar da Kain jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Bada Agajin Gaggawa Na Abinci, wanda aka gudanar a Fadar a Abuja, a ranar Alhamis.

Ya ce Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin cewa “a yi duk abin da ake buƙata don samar da abinci.”

Matakin dai ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin ya yi, dangane da zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran ƙalubalen tattalin arziki.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?