Back

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen Tukur Mamu da wasu mutane 14 a matsayin masu bayar da kuɗaɗen ta’addanci

Tukur Mamu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunan Tukur Mamu, wani mawallafi da ke Kaduna, da wasu mutane 14 a matsayin masu bayar da kuɗaɗen ta’addanci a ƙasar nan.

Mamu yana hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tun watan Satumban 2022.

An bayyana hakan ne a cikin wata takarda da Hukumar Kula da Harkokin Kuɗi ta Nijeriya (NFIU) ta fitar a ranar Talata.

Masu bayar da kuɗaɗen ta’addancin da aka gano sun haɗa da mutane tara da ma’aikata da kamfanoni shida na ‘Yan Canjin Kuɗi (BDC).

NFIU ta yi nuni da cewa, Kwamitin Takunkuma na Nijeriya ya gana a ranar Litinin, inda aka ba da shawarar ƙaƙabawa wasu takamaiman mutane da hukumomi takunkumi sakamakon zarginsu da hannu wajen bayar da kuɗaɗen ta’addanci.

NFIU ta bayyana cewa, Mamu na da hannu wajen bayar da kuɗaɗen ta’addanci ta hanyar karɓa da kuma kai kuɗaɗen fansa fiye da dala 200,000 don tallafa wa ‘yan ta’addar ISWAP domin sako mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

Ta bayyana cewa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, tare da amincewar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da sunayen mutane da kamfanoni da za a sanya a cikin jerin sunayen Takunkuman Nijeriya.

Wani mai bayar da kuɗaɗen ta’addanci, a cewar NFIU, shi ne wanda ake zargi da kai hari cocin St. Francis Catholic Church a Owo, hedikwatar ƙaramar hukumar Owo ta jihar Ondo a ranar 5 ga watan Yuni, 2022, da kuma Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja a ranar 5 ga Yuli, 2022.

Wani kuma shi ne “ɗan ƙungiyar ta’addar Ansarul Muslimina Fi Biladissudam, ƙungiyar tana da alaƙa da Al-Qaeda a yankin Magrib.”

“An horar da mutumin kuma ya yi aiki a ƙarƙashin Muktar Belmokhtar, wanda aka sani da One Eyed Out, ya jagoranci Al-Murabtoun Katibat na AQIM a Aljeriya da Mali,” inji ta.

NFIU ta ce mutumin “ya ƙware wajen tsara sadarwar ɓoye ta ‘yan ta’adda kuma shi ma ƙwararre ne na na’urar fashewa.

Ya ce: “Mutumin kuma mai tsaron ƙofa ne ga shugaban ANSARU, Mohammed Usman wanda aka sani da Khalid Al-Bamawi.

“Hakazalika, shi masinja ne kuma jagorar tafiya zuwa AQIM Katibat a cikin hamadar Aljeriya da Mali. Yana aikin kafinta. Mutumin ya gudu daga Gidan Gyaran Hali na Kuje a ranar 5 ga Yuli, 2022. A halin yanzu ba a kamo shi ba.”

An kuma bayyana wani babban kwamandan Daular Islama ta Yammacin Afirka Okene a matsayin mai bayar da kuɗin ta’addanci.

NFIU ta lura cewa mutumin ya shahara a shekarar 2012 a matsayin reshen Arewa ta Tsakiya na Boko Haram.

“Ana zargin ƙungiyar da hare-haren da aka kai a kusa da Babban Birnin Tarayya da kuma shiyyar Kudu maso Yamma, ciki har da harin da aka kai ranar 5 ga watan Yunin 2022 a cocin St. Francis Catholic Church, Owo, jihar Ondo,” inji ta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?