
Gwamnatin Najeriya ta buƙaci taimakon Hukumar ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (INTERPOL) domin farauto tare da kame wasu mutane uku da ake tuhuma bisa zargin fitar da dala miliyan shiga da dubu ɗari biyu daga Babban Bankin Najeriya CBN ta hanyar wata takarda ta jabu.
Ofishin Mai Bincike na Musamman na CBN, Jim Obazee ne ya buƙaci hakan a ranar Litinin bayan da ya samu odar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ofishin, ta wata wasiƙa da Shugaban Gudanarwa ta, Eloho Okpoziakpo, ya bayyana sunayen waɗanda ake tuhuma da Adamu Abubakar, Imam Abubakar da Odoh Ochene.
A baya dai Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta tuhumi Mista Ochene, wanda ba a kama ba, tare da tsohon Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, da laifin satar waɗannan kuɗaɗe da cewa fadar Shugaban Ƙasa ce ta buƙaci a biya masu sa ido kan zaɓen ƙasa da ƙasa.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta yi zargin cewa a ranar 8 ga watan Fabrairun 2023, Mista Emefiele ya haɗa baki da Mista Ocheme domin karɓar kuɗi dala miliyan shida da dubu ɗari biyu daga bankin CBN, inda ya ce, Sakataren Gwamnatin Tarayya na wancan lokacin, Boss Mustapha ne ya buƙaci a biya kuɗin “ta wata wasiƙa mai kwanan wata 26 ga Janairu 2023 tare da Ref No. SGF.43/L.01/.”
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta kuma yi zargin cewa Mista Emefiele, a watan Janairun 2023, ya ƙirƙiri takarda mai suna: “ UMURNIN SHUGABAN ƘASA AKAN MANUFOFIN MASU SA IDO AKAN ZABE NA WAJE,” mai kwanan wata 26 ga Janairu 2023 tare da Ref No. SGF.43/L.01/201.
A cikin wasiƙar zuwa ga ‘yan sandan kasa da kasan, ofishin mai bincike na musamman na babban bankin CBN ya buƙaci Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa da Ƙasa da ta “sa ido” tare da sanya mutanen uku da ake zargi da gudu a cikin “jan sanarwa” da nufin kama su tare da mayar da su gida.
Tun da farko dai mai binciken na musamman ya samu sammacin kama waɗannan mutane uku daga Babbar Kotun Tarayya ta hanyar shigar da ƙarar da ta shigar a ranar 18 ga watan Janairu.
Dangane da buƙatar hukumar ta INTERPOL, hukumar ‘yan sandan ta kuma shigar da ƙara a tuhume-tuhume shida da ake buƙata domin farautar waɗanda ake nema ruwa a jallo.