Back

Gwamnatin Tarayya ta buga adadin Kuɗaɗen da aka rabawa jihohi a cikin shekarar bara

Gwamnatin tarayya ta fitar da duk wani kaso na wata-wata da aka rabawa matakai uku na gwamnatin Najeriya a shekarar bara (2023).

Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) ya ce ya buga dukkan kason da aka ware wa matakai uku na gwamnati domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Ofishin akanta Janar din ya yi wannan bayanin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Alhamis sha biyar ga watan nan na Fabrairu.

Bawa Mokwa, Daraktan Yada Labarai na Ofishin ya bayyana cewa: “Ana ci gaba da buga bayanan kudaden shiga na wata-wata da Kwamitin Kasafin Kudi na Tarayya (FAAC) ke raba wa bangarorin gwamnati uku.”

Mokwa ya ce: “Hukumar OAGF na da tafiya da zamani wajen buga rabon kudaden shiga na wata-wata, ya Kara da cewa wannan kokari ne da zai ci gaba da dorewa.

Yace, “A bisa tsarin ofishin Akanta Janar na tarayya wajen fadakar da ‘yan Najeriya game da kudaden gwamnati da kuma yadda ake kashewa, ofishin ya kammala buga rabon kudaden shiga na wata-wata na shekarar 2023.”

Ya ci gaba cewa, an buga rabon kudaden shiga na shekarar 2023 duk wata a cikin bugu da kafafen yada labarai na yanar gizo da kuma shafin ta na ta shafin irin wannan.

A cewar ofishin, an riga an buga cikakkun bayanai na kudaden shiga na Disamba 2023 wanda aka raba a watan Janairu 2024 akan yanar gizon ta.

Mokwa ya sha alwashin cewa ofishin akanta Janar din zai ci gaba da “tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin hada-hadar kudade na gwamnati tare da tabbatar da manufofin gudanar da hada-hadar kudi”.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?