A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da aikin kamfanin jiragen sama na Air Nigeria har zuwa wani lokaci.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan a wajen taron ministoci na murnar cika shekara ta farko na gwamnatin Tinubu.
Da yake bayyana dalilin dakatarwar, Keyamo ya ce kamfanin jirgin bai taɓa zama na Nijeriya ba, a maimakon haka, wani yunƙuri ne na kwaikwayon wani kamfanin jiragen sama na ƙasar waje da ke aiki a Nijeriya.