Back

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Jami’ar Obafemi Awolowo, da kewaye

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da ayyukan haƙar ma’adanai a harabar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife da kewaye har sai an kammala bincike kan ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a can.

Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake, ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan wata ganawa da Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Adebayo Bamire, da sauran manyan jami’an jami’ar.

A cewar Alake, biyo bayan rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke yi kan ayyukan masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a cikin harabar jami’ar, nan take ma’aikatar ta ɗauki matakin gano gaskiyar zargin.

“Bayan koke-koken da ake samu na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ko kuma zargin munanan ayyuka da masu haƙar ma’adanai a cikin OAU suke yi, nan take muka tura jami’an Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA), da kuma Hukumar Kula da Haƙar Ma’adanai domin tantance su a nan take. Rahotannin farko da suka zo min sun nuna cewa haƙiƙa an yi wasu ayyuka a kusa da harabar. Daga nan ne ma’aikatar ta dakatar da duk wasu ayyuka, na bisa doka ko kuma waɗanda suka saɓa wa doka, don ci gaba da bincike,” inji shi.

Alake ya ce biyo bayan gayyatar da wasu ma’aikatan da aka ce suna gudanar da ayyuka ba bisa doka ba a kewayen yankin, sun gabatar da wasu lasisi da wasiƙun amincewa wanda ya sa aka ci gaba da bincike don tabbatar da sahihancinsu; don haka ya zama wajibi a gayyato mahukuntan jami’ar domin gudanar da shari’a.

“Mun yi taro mai albarka, kuma an samu bayanai da yawa daga ciki. A bisa sakamakon taron, na sanar da dakatar da duk wasu ayyukan haƙar ma’adanai a harabar jami’ar, da asibitin koyarwa da kuma kewayen yankin da iyakokin jami’ar har zuwa lokacin da za a kammala cikakken bincike,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?