Back

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin tallafa wa tsaron yanar gizo

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin nan da aka ƙaƙaba wa masu ajiya a banki na tallafin tsaron yanar gizo.

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya bayyana shigo da harajin kan kuɗaɗen da jama’a da kamfanoni ke turawa, wanda hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana matakin da gwamnatin ta ɗauka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a Fadar Gwamnati da ke Abuja ranar Talata.

Ya ce ana yin nazari kan shirin. “Matsayin gwamnati shi ne an dakatar da wannan shirin. An ɗage shi. Matsayin gwamnati kenan a yanzu. Ana sake sabon nazari a kan sa.

“An yi maganar sosai a taron Majalisar (FEC) a jiya. Kun san cewa majalisar ta yau (taron) an ɗora ne kan na jiya,” inji ministan.

Ya ƙara da cewa: “Don haka, zan iya gaya maku cewa an dakatar da harajin tsaron yanar gizo. Gwamnati na sake tunani a kan sa.”

A ranar 6 ga watan Mayu ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna, masu gudanar da hada-hadar kuɗi ta wayar salula, da masu ba da sabis na biyan kuɗi da su aiwatar da wannan harajin kamar yadda yake ƙunshe a cikin Dokar 2024 ta Laifin Yanar Gizo (Hanawa, Rigakafi, da sauran su) (gyara).

An tsara za a riƙa biyan harajin kashi 0.5 cikin ɗari kan duk kuɗin da mutum ya tura wa wani. Za a aika da kuɗaɗen ne zuwa Asusun Ajiyar Tsaron Yanar Gizo na Ƙasa wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) ke shugabanta.

Sai dai matakin ya fusata mutane matuƙa, lamarin da ya sa ake kira da a dakatar da shi.

A makon da ya gabata ma Majalisar Wakilai ta buƙaci CBN da ya janye umarnin da ya ba bankuna da su fara aiwatar da harajin, inda ta bayyana hakan a matsayin “shubuha”.

Wannan matakin na gwamnati ya kasance a matsayin martani ga wani ƙudiri kan buƙatar gaggawa na dakatarwa da kuma gyara aiwatar da harajin tsaron yanar gizo da ɗan majalisa Kingsley Chinda ya gabatar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?