
Rikicin Zaɓen 2023
Gwamnatin Tarayya ta hannun Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta fara gurfanar da wasu ma’aikatan Hukumar Zaɓe Mai Zaman KANTA (INEC) da ‘yan jam’iyyar siyasa da ake tuhuma da laifuka daban-daban a zaɓen 2023.
Laifukan zaɓe na ci gaba da zama manyan barazana ga sahihin zaɓe a Najeriya, domin su kan haifar da tashin hankalin siyasa.
Bayan zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya ce Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) sun kama mutane sama da ɗari bakwai da suka saɓa wa dokokin zaɓe.
A ranar 2 ga watan Mayun 2023 ne INEC ta ce za ta gurfanar da mutane ɗari biyu da sha biyar da hukumar NPF ta miƙa mata daga cikin mutane ɗari bakwai da saba’in da huɗu da hukumar ta kama bisa laifuka daban-daban da suka shafi zaɓe a lokacin zaɓen.
Hukumar INEC ta ce tana haɗin gwiwa da hukumar NBA, wadda za ta yi ayyukan shari’a kyauta don tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata laifukan zaɓe.
Daga cikin ƙararraki ɗari biyu da sha biyar da INEC ta samu, ƙararraki ɗari da casa’in da shida laifukan zaɓe ne kuma INEC da NBA ne ke gudanar da su.
Sakataren Yaɗa Labarai na NBA, Habeeb Lawal, ya shaida a ranar Juma’a cewa, ana tuhumar mutane ɗari da casa’in da shida da suka haɗa da jami’an INEC da ‘yan jam’iyyun siyasa da laifuka daban-daban da suka haɗa da siyan ƙuri’u, mallakar makamai, da sauran su a zaɓen 2023.
Lawal ya bayyana cewa ana gudanar da ƙarar ne a ƙananun kotuna da kuma manyan kotunan jihohi da kuma babban birnin tarayya.
Ya bayyana cewa, “Jimillar mutane ɗari da casa’in da shida ne ake tuhuma da laifuka daban-daban waɗanda ’yan sa kai na Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya ne ke gudanar da gurfanarwar kyauta.”
Laifukan sun haɗa da rashin yin aiki, haɗa baki wajen aikata laifi da rashin gaskiya a wuraren zaɓe, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba a ranar zaɓe, ƙwace da lalata kayayyakin INEC, rashin yin aikin zaɓe da kyau, mallakar kayan zaɓe ba bisa ƙa’ida ba, jawo masu zaɓe da sayen ƙuri’u, ɓarna da kai farmaki, da tashin hankalin zaɓe.
“Wasu daga cikin waɗanda ake zargin jami’an INEC ne, yayin da wasu ‘yan jam’iyyar siyasa ne da kuma mutanen da ba su da wata alaƙa ta siyasa.
“Ƙananun kotuna da manyan kotunan jihohi da na babban birnin tarayya suna da hurumin shari’ar laifukan zaɓe bisa ga Dokar Zaɓe.
“Saboda haka ‘yan ƙungiyarmu suna gabatar da shari’ar laifukan a waɗannan kotuna daban-daban a faɗin ƙasar nan, domin da wuya akwai wata jiha ta tarayya da ba a gudanar da shari’ar.”
Da aka tambaye shi ko wane irin tasiri shari’ar za ta yi kan zaɓukan da za a yi a nan gaba, sakataren yaɗa labaran ya ce, “Mun yi imanin cewa samun nasarar gurfanar da masu laifin zaɓe zai hana mutanen da ke da burin shiga muƙaman siyasa ido rufe.
“Muna da fatan cewa wannan ƙoƙarin zai yi tasiri da tsaftace tsarin zaɓe da al’adunmu.”
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban Hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana cewa hukumar ba za ta lamunci munanan ɗabi’u ba, inda ya ƙara da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata laifin a nan gaba kan abin da suka aikata.
Oyekanmi ya ce, “Ta hanyar haɗa hannu da Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya wajen gurfanar da waɗanda suka aikata laifukan zaɓe a gaban kotu, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta tana ƙarfafa ƙudurin ta na ƙin amincewa da munanan halaye.
“Babban saƙonmu ne ga masu son aikata laifin cewa za a tuhume su da abin da suka aikata.
“Yayin da muka samu wasu matakai na nasara wajen gurfanar da masu laifin zaɓe a baya, tayin da NBA ta yi na taimaka mana kyauta zai ƙara faɗaɗa fage kuma ya zama jan kunne ga wasu.”
Babban Darakta na Cibiyar Bayar da Shawarar Doka ta Ƙungiyoyin Jama’a, Auwal Rafsanjani, ya bayyana cewa Najeriya za ta fita daga tashe-tashen hankula da cin hanci da rashawa idan aka yi maganin masu aikata laifin zaɓe.
Ya ce, “A matsayin hanyar tsaftace tsarin zaɓe, dole ne a sanya takunkumi ko hukunci ga mutanen da suka karya dokar mu.”