Back

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon hatsi tan 42,000 a Sokoto

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, da Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto, yayin ƙaddamarwar

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin fitar da tan 42,000 na kayayyakin abinci iri-iri daga Ma’ajiyar Abinci ta Ƙasa (NSFR), a faɗin ƙasar nan.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Suleiman Haruna, ya fitar a ranar 8 ga Afrilu, 2024.

Sanarwar ta ce Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, da yake jawabi a taron ƙaddamarwar a ranar Lahadi, 6 ga Afrilu, 2024, a gidan gwamnati dake Jihar Sokoto, ya bayyana cewa rabon hatsin wani ɓangare ne na shirin shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa don rage wahalhalun da ke cikin ƙasar da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya domin samun ci gaba mai ɗorewa da wadata ga dukkan ‘yan ƙasa.

Ministan ya ce, Shugaban Ƙasa Tinubu ya damu da hauhawar farashin kayan abinci, kuma ya ƙuduri aniyar samar da muhimman abinci da kuma araha ga ‘yan Nijeriya, dalilin da ya sa ya amince da raba tan 42,000 na hatsi iri-iri da suka haɗa da dawa, gero, da masara, da tan 60,000 na shinkafa ta hanyar masu sarrafa shinkafa.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta tunanin cewa sauye-sauyen Shugaban Ƙasa ba zai zo da raɗaɗi ba. Duk da haka, akwai tabbaci cewa, a cikin dogon lokaci, ƙarshen zai tabbatar da hanyoyin.

“Gwamnati ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri da fahimta yayin da muke matsawa cikin waɗannan lokuta masu wahala zuwa wani yanayi mai ɗimbin fa’ida da sabon fata. Kamar yadda Shugaban Ƙasa ke nanatawa, waɗannan matsaloli da muke fuskanta na wucin gadi ne, kuma tabbas za mu shawo kan su,” inji shi.

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya ce Shugaban Ƙasar na da burin rage raɗaɗin tashin farashin kayayyakin masarufi ta hanyar tabbatar da dawwamammen tanadi, kamar yadda Tsarin Adana Abinci na Nijeriya ya tanada.

Ya bayyana cewa, ana sa ran Ma’ajiyar Abinci ta Ƙasa za ta adana kashi 5 na adadin abincin da ake nomawa a duk shekara, yayin da ake sa ran Gwamnatocin Jihohi za su ajiye kashi 10 a matsayin kayayyakin da za su cika Ma’ajiyar Ƙasa; duk da haka, kayayyakin sun kasance babu su a yawancin jihohin Tarayyar kuma hakan ya ci gaba matsin lamba a kan kayayyakin Ma’ajiyar Abinci na Ƙasa na Gwamnatin Tarayya, musamman a lokuta irin wannan.

Ya ce, “Saboda haka, ina so in ƙarfafa wa dukkan gwamnatocin jihohi gwiwa da su fara ajiye kayayyakin a jihohinsu daban-daban, saboda buƙatar gaggawa nan gaba, za su sami kayayyaki wanda zai cika ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya.”

Ya kamata a lura da cewa tan 42,000 na kayan abinci iri-iri, wanda ya ƙunshi masara (tan 23,600), dawa (tan 12,860), gero (tan 3,700), da Garri (tan 1,840), za a raba wa ƴan Nijeriya masu rauni.

Kason na jihar Sokoto ya ƙunshi masara tan 506.00, dawa (tan 589.00), da gero (tan 216.20), (manyan motoci 44.01 ko buhu 26,406 na 50kg) kuma tuni aka kai wa Jihar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?