Back

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon hatsi tan 42,000 kyauta, kuma za ta fitar da shinkafa tan 58,500 zuwa kasuwanni

Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta ce an fara rabon tan 42,000 na hatsi iri-iri a faɗin ƙasar nan.

Ta kuma ce an kusan kammala shirye-shirye don fitar da ƙarin tan 58,500 na niƙaƙƙen shinkafa daga manyan masu niƙan shinkafa zuwa cikin kasuwanni, don ingantacciyar daidaitawa.

Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da Majalisar Dattawa ta hannun Kwamitinta na hadin gwiwa Kan Ayyukan Noma da Raya Karkara.

Tattaunawar wani ɓangare ne na matakan samun amsa kan hanyoyin da Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da su wajen fita daga matsalar abinci ta ƙasa, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ƙasar ke fuskanta.

Kwamitin wanda Sanata Saliu Mustapha (APC Kwara ta tsakiya) ya jagoranta, a wata ganawa da ministan, ya yi tambayoyi game da shirin Gwamnatin Tarayya na daƙile tsadar kayan abinci a ƙasar nan da kuma samar da sauƙi da wadata ga talakawa.

Da yake mayar da martani ga binciken ‘yan majalisar, ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara rabon tan 42,000 na hatsi zuwa wasu wuraren zama na manyan jihohin ƙasar baki ɗaya.

Ya ce: “Mun sami umarni da izini daga Shugaban Ƙasa don a rarraba tan 42,000 na hatsi iri-iri kyauta ga al’ummar Nijeriya nan take.

“An karɓi wannan (a) tsakiyar watan Fabrairu. A yayin da muke magana, muna da bayanan yadda ake rabon kayan, amma zan so in roƙi Majalisa da manyan Sanatoci cewa ba za a iya bayyana wasu matakan ba. Amma jihohi da dama sun fara karɓar hatsinsu.

“Tun farko muna raba wa manyan jihohin ƙasar nan, domin duk kuna sane da haɗarin da ke tattare da lalata kayan abinci. Don haka muna aiki tare da Ofishin Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA) da sauran hukumomin tsaro na ƙasa.

“Bugu da ƙari, za a fitar da tan 58,500 na niƙaƙƙen shinkafa daga manyan masu niƙan shinkafa cikin kasuwa don daidaitawa”, inji shi.

Ministan ya kuma ce matakan da ake ɗauka sun zama dole domin rage tasirin wahalhalu ga ‘yan Nijeriya wanda ya ce nan ba da jimawa ba za su zama tarihi.

Don dalilai na tsaro, ya sanar da mambobin kwamitin cewa ma’aikatar tare da ONSA sun haɗa kai don magance al’amuran da suka shafi lalata wuraren ajiyar kayan abinci a faɗin ƙasar.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman tattaunawa, shugaban kwamitin, Sanata Mustapha, ya bayyana jin daɗinsa da matakan da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka.

Ya ce : “Daga zaman mu na tattaunawa, mu a ɓangaren majalisar, muna da cikakken bayanin abubuwan da ke faruwa, mun gamsu cewa matakin da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka yana kan hanyar da ta dace.

“Abin da muka sake yi shi ne mun ƙara jaddada buƙatar yin wasu abubuwa kan lokaci, ina ganin daga wannan tsarin haɗin gwiwa, da yardar Allah, ‘yan Nijeriya za su ƙara fahimtar tsarin gwamnati kan samar da abinci.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?