Back

Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Ƙungiyar Ƙwadago don ci gaba da tattaunawa ranar Juma’a kan mafi karancin albashi

Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago za su ci gaba da tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa a ranar Juma’a, 31 ga Mayu, 2024.

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya tabbatar da faruwar hakan biyo bayan wata wasiƙar gayyata daga shugaban kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Kwafin wasiƙar yana ɗauke da sa hannun Sakataren Kwamitin, Ekpo Nta.

Ajaero ya tabbatar da cewa ƙungiyoyin ƙwadago za su mutunta gayyatar, inda ya ce “e, za mu halarta amma kun san wa’adin mu zai ƙare ranar Juma’a. Idan sun gabatar da mafi kyawun tayi ranar Juma’a za mu karɓa.”

Idan za a iya tunawa dai tattaunawar da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ba ta yi nasara ba a ranar Talata bayan da gwamnati da Ƙungiyoyin Sashin Masu Zaman Kansu (OPS) suka ƙara tayin su zuwa naira 60,000.

Gwamnati ta ƙara naira 3,000 a farkon tayin naira 57,000 da ta gabatar a makon da ya gabata, inda adadin ya kai naira 60,000, amma ƙungiyar kwadago ta ki amincewa da hakan a taron.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?