Back

Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Sheikh Gumi don amsa tambayoyi kan ayyukan ‘yan bindiga

Sheikh Gumi

Gwamnatin Tarayya ta ce ta gayyaci malamin addinin Islama na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, kan kalaman da ya yi kan ayyukan ‘yan bindiga a ƙasar nan.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja.

Idris ya ce Gumi bai fi ƙarfin doka ba, yana mai cewa gwamnati ta ga ya dace ta gayyace shi domin amsa tambayoyi.

Ƙarin bayani ba da jimawa ba…

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?