Back

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da shugaban Miyetti Allah kan zargin ta’addanci

Shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja bisa zarginsa da aikata laifukan ta’addanci.

A cikin tuhume-tuhume uku da Gwamnatin Tarayya ta karanta masa a jiya, Gwamnatin Tarayya ta zargi Bodejo da kafawa da tallafa wa wata ƙabilar soji ba bisa doka ba, Ƙungiyar Zaman Lafiya da ke Jihar Nasarawa, wanda ya saɓa dokar hana ta’addanci ta 2011. Sai dai Bodejo bai amsa laifin ba.

Biyo bayan da ya ce ba shi da laifi, Mai shari’a Inyang Ekwo ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraren ƙarar.

Alƙalin ya kuma bayar da umarnin tsare wanda ake tuhuma a hannun Hukumar Leƙen Asiri ta Tsaro (DIA).

Shugaban na Miyetti Allah dai ya kasance a tsare ne biyo bayan kafa rundunar mutane 1,144 a ranar 17 ga watan Janairu, wanda ya yi iƙirarin don magance duk wani nau’in rashin tsaro kamar na ‘yan bindiga da satar shanu ce.

Kafin a gurfanar da shi gaban kuliya, Bodejo ya shigar da ƙara a gaban kotu inda ya ke ƙalubalantar ci gaba da tsare shi ba tare da tuhumar sa ba.

Hakan ne ya tilasta wa alƙalin, yayin da yake sabunta ci gaba da tsare shi, ya umurci Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da ta shigar da ƙarar Bodejo cikin kwanaki bakwai.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?