Back

Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar da ake yiwa Shugaban Miyetti Allah, Bodejo na ta’addanci

A ranar Laraba ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta wanke Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Kore, Alhaji Bello Bodejo, daga tuhumar da ake masa na ta’addanci da ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, AGF, ya shigar a kansa.

Mai Shari’a Inyang Ekwo, a wani ɗan taƙaitaccen hukunci, ya sallami Bodejo bayan da lauyan AGF, Aderonke Imana, ta gabatar da buƙatar a janye tuhume-tuhumen uku.

Da aka ci gaba da sauraron ƙarar, Imana ta sanar da kotun cewa ta yi neman ne ta baka.

Lauyan ta ce buƙatar ta yi daidai da Sashe na 108 na Dokar Shari’a ta ACJA, 2015.

Ta ce buƙatar ta ƙara yin nuni da ƙarfin ikon AGF a ƙarƙashin Sashe na 174 na kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara).

“Saboda haka, Mai Girma Atoni-Janar na Tarayya ya umarce ni da in janye wannan tuhumar da ake yi wa wanda ake tuhuma domin adalci.

“Wannan ita ce buƙatar mu,” inji ta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?