Back

Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin Binance na neman cin hanci

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris

Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan iƙirarin da Shugaban kamfanin Binance, Richard Teng, ya yi na cewa wai wasu jami’an gwamnatin Nijeriya sun buƙaci a ba su cin hanci da kuɗaɗen kirifto don warware binciken laifuffukan da ake yi wa masa.

Teng ya yi wannan iƙirarin ne a wani shafin yanar gizon da kafafen watsa labarai na ƙasashen waje suka buga ranar Talata, inda ya ƙara da cewa lauyan Binance ya ƙi amincewa da tayin.

Da yake mayar da martani kan zargin a ranar Laraba, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Teng ya ƙare da “dabarun karkatar da hankulan jama’a da kuma yunƙurin yin ɓatanci da kamfanin ke yi don kawar da tuhume-tuhume masu tsanani da yake fuskanta a Nijeriya.”

A wata sanarwar da Rabiu Ibrahim, mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai ya sanya wa hannu, ministan ya jaddada cewa wanda ya kafa Binance, Changpeng Zhao, ya aikata irin wannan laifin na halasta kuɗaɗen haram a Amurka, kuma a halin yanzu yana zaman gidan yari, lamarin da ke nuni da cewa ya kamata kamfanin na kirifto ya miƙa kan sa ga hukuma domin bincike.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta na sane da yunƙurin da Binance ke yi na wanke sunan sa a matsayin kamfanin da ba ya bin ƙa’ida da dokokin da ke jagorantar harkokin kasuwanci a ƙasashe masu cin gashin kai.

“A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafin yanar gizon da yawancin kafafen watsa labarai na ƙasa da ƙasa suka wallafa a yanzu, Shugaban Binance Richard Teng, ya zargi kan wasu jami’an gwamnatin Nijeriya da ba a san ko su waye ba da cin hanci da rashawa, wanda ya yi iƙirarin cewa sun buƙaci a biya kuɗaɗen kirifto dala miliyan 150 don warware binciken laifuffukan da ake yi wa kamfanin.

“Wannan iƙirarin na Shugaban Binance ba gaskiya ba ne. Ba komai ba ne illa dabarar karkatar da hankulan jama’a da kuma yunƙurin yin ɓatanci da kamfanin ke yi don kawar da tuhume-tuhume masu tsanani da yake fuskanta a Nijeriya.

“Gaskiyar wannan al’amari ita ce ana binciken Binance a Nijeriya ne saboda yadda ya ba da damar yin amfani da dandalin sa wajen halasta kuɗaɗen haram, bayar da tallafi ga ta’addanci, da kuma tafka maguɗin kuɗaɗen ƙasashen waje ta hanyar cinikin haramun.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?