Back

Gwamnatin tarayya ta rufe shahararren kantin sayar da kayayyaki a Abuja kan farashin ƙarya

A ranar Juma’ar ne Hukumar Gasa da Kare masu siyan kaya ta Tarayya, FCCPC ta rufe Sahad Store, wani shahararren kantin sayar da kayayyaki da ke unguwar Garki a Abuja.

Hukumar ta ta ce an rufe shagon ne saboda rashin nuna gaskiya kan yadda yake ƙayyade farashin kayayyaki.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i ashirin da huɗu bayan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana shirye-shiryen magance matsalolin da ke haddasa matsalar ƙarancin abinci a faɗin ƙasar nan.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar gwamnonin jihohi suka amince da kafa wani kwamiti da zai magance matsalar ɓoye kayayyakin abinci a ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan bayan ganawar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi da gwamnoni da shugabannin hukumomin tsaro da wasu ministoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis.

Idris, wanda ya zargi wasu ‘yan kasuwa da tara kayan abinci, ya bayyana cewa an ba wa hukumomin tsaro damar haɗa kai da gwamnoni don magance matsalar.

“Shugaban Ƙasa ya amince da kafa wani kwamiti don zurfafa tattaunawar da aka yi a taron da aka kammala. Tabbas kun san cewa ba zai yiwu a iya kammala yawancin batutuwan da aka taɓo a taron ba don haka za a ci gaba da zama.

“An umurci Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Darakta Janar na ma’aikata na jiha, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da su haɗa kai da gwamnonin jihohi domin duba lamarin masu tara kaya.

“A wannan lokaci, al’umma na buƙatar a kawo wa jama’a abinci domin mu iya rage farashi da kuma ɗora abinci a kan teburin yawancin ‘yan Najeriya. Sauran masu sayar da kayayyaki sun shagaltu da tara waɗannan kayayyaki domin ‘yan Najeriya su sha wahala ko kuma su ƙara samun kuɗi a sakamakon haka.

“Don haka gwamnoni da shugaban ƙasa sun ɗauki wannan matakin cewa hukumomin tsaro za su haɗa kai da gwamnonin jihohi don ganin hakan ya zo ƙarshe.”

Sai dai gwamnatin tarayya ta zargi mahukuntan Sahad Store da zambatar kwastomomi ta hanyar cajin su farashi saɓanin farashin da ke kan katako na ajiye kaya.

Tawagar aikin ta samu jagorancin Muƙaddashin Shugaban Hukumar, Adamu Ahmed Abdullahi. Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan rufe kantin, Abdullahi ya bayyana cewa binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa masu gudanar da babban kantin suna zambatar abokan ciniki.

Hukumar ta bayyana cewa, kantin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike, inda ta ce, “Abin da muka gano cewa waɗannan mutane suna yi shi ne yaudara wurin sanya farashi da kuma rashin gaskiya a sanya farashin, wanda ya saɓa wa sashe na 115 (3) na dokar hukumar da ta ce ba a buƙatar mabuƙaci ya biya farashi na kowane kaya ko sabis fiye da wanda ke kan nuni.”

“Sashi na 155 ya bayyana cewa duk wani kamfani da ya saɓawa doka yana da tarar naira miliyan ɗari ko ma fiye da haka kuma daraktocin kamfanin da kansu suna da alhakin biyan naira miliyan goma kowanne ko kuma ɗaurin watanni shida ko kuma duka biyun.

“Abin da muka yi a yau shi ne mu tabbatar sun bi doka. Da farko mun kira su don su zo su kare kansu amma ba su zo ba. Daga baya sai suka aika da lauya wanda muka tambaye shi ko ya san gaskiyar lamarin. Yace bai sani ba.

“Don buɗe kantin, dole ne su tabbatar da cewa sun yi abin da ake buƙata a yi.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?