Back

Gwamnatin Tarayya ta sake ƙara kuɗin wutar lantarki

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta ba da umarnin ƙara farashin wutar lantarki a ƙasar nan take daga ranar Laraba 3 ga watan Afrilu.

Mataimakin Shugaban NERC, Musiliu Oseni, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Mista Oseni ya ce za a sanya sabon farashin ne kawai ga masu amfani da wutar lantarki waɗanda ke wakiltar kashi 15 na al’ummar ƙasar amma suna amfani da kashi 40 na wutar lantarkin kasar.

Hukumar NERC, a watan Janairu, ta ce gwamnatin Nijeriya za ta biya kusan naira tiriliyan 1.6 don tallafa wa wutar lantarki a shekarar 2024.

Cikakkun bayanai daga baya…

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?