Back

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita hutun Ƙaramar Sallah

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 11 ga Afrilu, 2024, a matsayin ƙarin ranakun hutun Ƙaramar Sallah.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Aishetu Ndayako, wanda aka raba a shafin ma’aikatar na X a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta amince da ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ƙarin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah na bana.

“Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, yayin da yake taya al’ummar musulmi murnar kammala watan Ramadan lafiya, ya nanata ƙudurin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na samar da tsaro da wadata a Nijeriya don ci gaban kowa da kowa.”

A ranar Litinin ne Saudiyya ta ce ba a ga jinjirin watan Shawwal ba, wanda hakan ke nuna cewa za a ci gaba da azumin ranar Talata.

Haka kuma ta ƙara da cewa za a gudanar da Ƙaramar Sallah ne a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu domin ganin an shiga sabon watan Musulunci.

Tun a ranar Lahadi ne Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024, a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Ƙaramar Sallah.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?