Back

Gwamnatin Tarayya ta yabawa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles game da nasarar da suka yi kan kasar Afirka ta Kudu

Gwamnatin Tarayya ta yabawa Super Eagles kan nasarar da suka yi akan kungiyar kwallon kafa ta Bafana Bafana ta kasar Afirka ta Kudu a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) 2023 da aka yi a kasar Ivory Coast.

An tashi wasan da ci 1-1 bayan karin lokaci, kuma kungiyar kwallon kafa mai rike da kofin sau uku za ta kara da mai masaukin baki Ivory Coast ko Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a wasan karshe a ranar Lahadi.

Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallo a ragar Najeriya a bugun fenareti 4-2 a gasar cin kofin nahiyar Afirka a ranar Laraba a Bouake.

Jim kadan bayan kammala wasan, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya bayyana nasarar da Super Eagles ta samu a matsayin babban ci gaba ga kasa Najeriya.

Yace “Dukkan al’ummar kasar nan na goyon bayan ‘yan wasan Super Eagles yayin da suke shirin kafa tarihi da rubuta sunayensu a gasar kwallon kafa ta Afirka da ta duniya baki daya.”

Ministan a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim ya fitar ya Kara da cewa “Idris ya ce yayin da ‘yan wasan Super Eagles ke sa ran zuwa wasan karshe, al’ummar kasar da gwamnati sun tsaya kyam a bayansu tare da basu kwarin gwiwar na ganin sun samu nasara da kuma sake dawo da kofin gasar cin kofin Afrika Gida Najeriya.”

Ministan wanda ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba wa Super Eagles goyon baya da kuma taya su murna a yayin da suke kokarin ganin sun yi nasara a wasan karshe, ya jaddada cewa kungiyar na dauke da fata da muradin daukacin al’ummar kasar a wuyansu.

Da nasarar ta ranar Laraba, Super Eagles za ta kara da mai masaukin bakin Ivory Coast ko Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, wadanda za su hadu daga baya, a wasan karshe a ranar Lahadi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?