Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar sanya takunkumi ga manyan makarantun da suka saɓa wa ƙa’idar tarayya wajen ɗaukar ma’aikata, inda ta dage cewa hakan ya zama tilas.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Sadarwa na Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta Tarayya (FCC), Dakta Chuks Okoli ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja cikin wata sanarwa.
Ya ƙara da cewa hukumar ta lura da takaicin yadda a yanzu wasu manyan makarantun tarayya suka fara aikin ɗaukar ma’aikata ba tare da bin ƙa’idar hukumar FCC da ke da alhakin tabbatar da daidaito da adalci bisa sashe na 14 (B) na kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Ya yi nuni da cewa takardar da aka fitar daga ofishin SGF ba ta ce kada makarantun tarayya su bi Ƙa’idar Ɗa’ar ta Tarayya ba.
“Saboda haka, dole ne kowace jami’a ta tarayya da ke ɗaukar ma’aikata ta bi ƙa’idojin FCC. Don guje wa shakku, da fatan za a duba littafin jagorar hukumar. Duk wani mutum, MDA ko jami’ar tarayya, da ke aiwatar da ɗaukar ma’aikata ba tare da bin ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata na FCC ba, zai yi laifi a ƙarƙashin sashe na 14, wanda za a hukunta shi a ƙarƙashin sashe na 15 na dokar,” inji Okoli.