Back

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da yankin mu wajen rabon manyan ayyuka, inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta sake jaddada damuwarta kan yadda aka yi watsi da yankin wajen rabon manyan ayyukan Gwamnatin Tarayya.

A jawabin da ya bayar a ƙarshen Taro na 10 na Ƙungiyar da aka gudanar a Bauchi, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, wanda shi ne Shugaban, ya ce yankin ma ba ya cikin shirin samar da ababen more rayuwa na ƙasa don sauya sheƙa daga man fetur zuwa iskar gas.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa, duk da kukan da take tayi na ganin an mai da hankali kan yanayin ababen more rayuwa a yankin wanda ake ta bayyanawa a duk tsawon shekarun da suka gabata, musamman rashin kyawun hanyoyin mota da hanyoyin jiragen ƙasa a kan hanyoyin tattalin arziƙi da suka haɗa yankin Arewa maso Gabas da sauran ƙasar, babu wani abu da ake ganin yana faruwa.

“Hanyoyin Enugu zuwa Maiduguri suna cikin mawuyacin hali kuma an lalata titin jirgin ƙasa daga Enugu zuwa Maiduguri. Wannan wata babbar hanya ce ta kasuwanci a yankin kuma tana da matuƙar muhimmanci ga haɗin kai, samar da zaman lafiya da inganta haɗin kan ƙasa.

“Ƙungiyar tana kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba halin da ake ciki tare da yin la’akari da sake gina waɗannan muhimman ababen more rayuwa tare da hanyar tattalin arziƙin Enugu zuwa Maiduguri da shigar da Arewa maso Gabas a cikin dukkan shirye-shirye da Tsare-tsare na Ci Gaban Ƙasa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?